kisan kalar namijin da zakiyi soyayya dashi

Ki san da irin mazan da zaki yi soyayya,ki lura da irin wadannan mazan domin a cikkin su akwai wadanda badon Allah zasu zo wajan ki ba,sai don wata manufar su daban,idan har kika bari suka rinjaye ki zasu tafi kuma su barki a bbu mai auran ki a cikin su.

 Akwai wadanda su ba mutanan kirki bane,daga lokacin daya zo wajan ki ki lura dashi da kuma kalaman sa a gare ki,karki yarda yana miki wasu kalaman batsa da sunan wai soyayyah ne,karya yake miki babu wani soyayyah a wajan sai ma son bata miki rayuwa da zaiyi.

 Kisan cewa namijn kwarai baya gwada tarbiyya mace ta irin wannna hanyar,domin akwai wasu masu cewa wai gwada ki sukeyi bbu wani gwaji,inda zaki bashi dama bata miki rayuwa zaiyi ya gudu ya barki.

 Idan har zakina tarayya da irin wadannan shaidanun mazan nan to ki sani babu mai kallon ki da mutunci,kuma kowa zai dauka ke irin su ne,namijin kwarai bazai zo ma wajan ki ba.

 Lallai ki lura da rayuwar ki,ki kare mutunci ki,ki kare mutuncin iyayen ki,ki kare mutuncin 'ya'yan ki, idan har kin gina rayuwar ki mai kyau kin kyautatawa wa zuri'ar ki, idan kuma kin wulakanta rayuwar ki kin bar wa zuri'ar ki abin kunya har abada sai an fadi abinda kika aikata a rayuwar ki.

 Kar ki yarda mazan banzan nan su yaudare ki da raunin ki,domin mace akwai rauni ki tsare kan ki,ki zama mutuniyar kirki.

 Kuma yanayin shigar ki shi zaina kawo miki irin wadannan mazan,idan sunga kinyi shigar banza zasu san wannna irin su ce,ammma idan kina kiyaye wa Alllah zai miki tsari da irin wadannan mazan.

 Kar dadin duniya yana rudar da rayuwar ki har kina aikata abubuwa marar kyau.

 Addu'a ta Allah ya kare dukkan wata mace daga irin wadannan mazan.


Comments

Popular posts from this blog

mazan yanzu suncika yaudara